Gwamnatin Buhari ta amince a saki Biliyan 80 domin hanyar Legas zuwa Ibadan

Gwamnatin Buhari ta amince a saki Biliyan 80 domin hanyar Legas zuwa Ibadan

- Ana sa rai a karasa hanyar Legas zuwa Garin Ibadan da aka yi

- An shirya ware Biliyan 80 domin gyaran Ibadan zuwa Shagamu

- Minista Fashola ya kara komawa an yi magana da ‘yan kwangila

Majalisar zartarwa na Ministocin Gwamnatin Buhari sun yi na’am da a ware kudi har Naira Biliyan 80 domin a karasa aikin hanyar Legas zuwa Ibadan. An cin ma wannan matsaya ne a makon jiya bayan zama da ‘yan kwangilar.

Gwamnatin Buhari ta amince a saki Biliyan 80 domin hanyar Legas zuwa Ibadan

Za a taba bangaren Ibadan zuwa Shagamu Inji Fashola

Kamar yadda mu ka samu labari daga Ministan ayyuka Babatunde Fashola, za a kashe wasu sababbin kudi Biliyan 80 domin gyara bangaren titin Garin Ibadan zuwa Shagamu. Ana yawan amfani da wannan babban titi wanda ta fi kilomita 80.

KU KARANTA: Abin da ya sa Buhari ke amfani da tsofaffin motoci

Babatunde Fashola ya bayyanawa manema labarai wannan bayan taron wancan makon da aka yi wanda Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranta a dalilin rashin Shugaba Buhari a kasar a wancan lokaci.

Haka kuma za a ware wani kudi domin aikin hanyar dogon Legas zuwa Kano. Bayan nan kuma za a saki Naira Biliyan 18 dai domin gyara wata gada a Legas. Akwai kuma ma dai wasu gadan da ake shirin gyarawa a Jihar Osun da kewaye.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel