Jihohin Legas da Kaduna ne gaba a sahun bashi a Najeriya

Jihohin Legas da Kaduna ne gaba a sahun bashi a Najeriya

Idan ana maganar bashi duk Najeriya yanzu babu kamar Jihohin Legas da Kaduna da kuma Jihar Edo. Mun kawo maku jerin Jihohin da su ke kan gaba a wajen cin bashi a halin yanzu a Kasar:

Ga Jihohin nan kamar haka:

Jihohin Legas da Kaduna ne gaba a sahun bashi a Najeriya

Jihar Legas ta fi kowace tarin bashi a Najeriya

1. Legas

Duk Najeriya babu Jihar da ta kai Legas tarin bashi sai dai Jihar na da dinbin arziki. Ana bin Legas kudin da sun haura Dala Biliyan 1.43 na bashin kasar waje. Kusan kashi 40% na bashin Jihohin Najeriya na wuyan Legas.

KU KARANTA: Za ayi zabe da na'ura mai kwakwalwa a Jihar Kaduna

2. Kaduna

Bayan Legas dai sai Jihar Kaduna a sahun masu cin bashi a Najeriya. Kashi 6% na bashin kasar waje da ke wuyan Jihohin Kasar nan yana kan Jihar Kaduna. Ana bin Kaduna bashin sama da Dala Miliyam 225 a yanzu haka.

3. Edo

Jihar Edo ce ta 3 a wannan sahu inda ta ke rike da kashi kusan 5% na bashin Jihohin kasar. Abin da ake bin Jihar Edo na bashin kasar waje yana daf da shiga Dala Miliyan 180.

Sauran Jihohin da ke kan gaba su ne Kuros Riba masu Dala Miliyan 141, sannan Jihar Ogun mai bashin Dala Miliyan 103.55 da kuma Bauchi mai bashin Dala Miliyan 97 da irin su Osun, Adamawa, Enugu da kuma Jihar Katsina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel