Umaru 'Yaradua: Me baya ta bari bayan shekaru takwas da rasuwarsa

Umaru 'Yaradua: Me baya ta bari bayan shekaru takwas da rasuwarsa

- An cika shekaru takwas da rasuwar Ummaru Yaraduwa

- An sami canjin siyasa sosai bayan mutuwar tasa

- Yayi jinyar kusan shekaru takwas kafin wannan lokaci

Umaru 'Yaradua: Me baya ta bari bayan shekaru takwas da rasuwarsa

Umaru 'Yaradua: Me baya ta bari bayan shekaru takwas da rasuwarsa

A shekarar 2010, war haka, aka sami labarin rasuwar shugaban kasa Ummaru Yaradua, wanda ya sha jinya a kasashen Jamus, Ingila da Saudiyya, kafin ya dawo gida, nan ma yayi jinyar watanni, a cutar da har yanzu ba kowa ya sani ba.

A lokacin mukin Ummaru Yar'aduwa, akwai abubuwa da yawa da a yanzu mutane sun manta da su, bari mu leka muga me zamu iya zakulo muku:

1. Man Fetur na N65 a lita daya

2. Dala na N140 ga Naira

3. Boko Haram ta fara kai hare-hare a Arewa a 2009.

4. An sami sulhu a Neja Delta

DUBA WANNAN: Albarka na sanyawa diyata bayan ta musulunta

5. Yayi kokarin shiryawa da shugaba Buhari na jam'iyyar adawa

6. Ya kori El-Rufai da Ribadu hutun dole a kasar waje ta hanyar matsar siyasa

7. Ya so ya kawo teku arewa domin shigo da mai da kayan abinci ta hanyar yashe ruwan Neja

8. Ummaru Yaraduwa so yayi ya huta bayan yayi gwamna amma shugaba Obasanjo ya makala masa son mulki

9. A kokarinsa na kyautatawa talakawa ya kwace matatun mai da aka siyar wa su Dangote, sai dai ashe hakan ba wata dabaarar kirki bace.

10. Da tuni ya zuwa yanzu ya gamma nasa mulkinsa ya bar GEJ ko waninsa ya gaje shi, musamman daga kabilun kudu a 2015.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel