Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke yayin Zabe a jihar Ekiti, Jakadun Zabe sun yi arangama

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke yayin Zabe a jihar Ekiti, Jakadun Zabe sun yi arangama

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, mummunan rikici ya barke da yayi sanadiyar dakatar da gudanar da zaben tantance dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Ekiti.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, da yawan wakilai sun kada kuri'un su yayin da wasu daga cikin wakilan jam'iyyar suka fara gunaguni akan Ministan Ma'adanan kasa, Kayode Fayemi, inda suke zargin sa da sabawa ka'idoji na gudanar da zaben.

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke yayin Zabe a jihar Ekiti, Jakadun Zabe sun yi arangama

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke yayin Zabe a jihar Ekiti, Jakadun Zabe sun yi arangama

Wakilan sun yi zargin cewa, akwai alamun tuggu da wakilan Ministan ke kullawa yayin gudanar da zaben saboda haka ba za samu lamunta ba inda suka bude wuta a kan dakatar da kada kuri'u.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci taron jam'iyyar APC a garin Daura

Cikin gaggawa wakilan suka dakatar da zaben yayin da wannan lamari ya sanya jami'an tsaro suka harba harsashai bisa saman iska domin kowa ya shiga taitayin sa da kuma manufar kare akwatunan zabe.

Kokarin shugaban kwamitin gudanar da zaben, Gwamna Tanko Al-Makura na jihar Nasarawa, na kwantar da wannan tarzoma bai wani tasiri har zuwa karfe 5.00 na yammacin yau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel