Yanzu-Yanzu: An yiwa 'Dan Takarar shugaban jam'iyyar APC kisan gilla a jihar Delta

Yanzu-Yanzu: An yiwa 'Dan Takarar shugaban jam'iyyar APC kisan gilla a jihar Delta

Jaridar Legit.ng ta samu rahoton kisan gilla da aka yiwa wani dan takarar shugaban jam'iyyar APC, Mista Jerimiah Oghoveta, na mazabar Jeremi dake karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta kamar yadda shafin The Punch ya ruwaito.

Oghoveta wanda bai wuci shekaru 30 a duniya ba ya yi gamo da ajali inda aka daba masa kaifi a wuyan sa yayin da ake gudanar da taron jam'iyyar APC na kowace mazaba dake fadin kasar nan a ranar yau ta Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa, wani dan uwa ga daya daga cikin shugabannin jam'iyyar na yankin shine ke da alhakin aikata wannan mummunan ta'addanci.

Sai dai gunanin al'ummar yankin sun bayyana cewa har yanzu ba bu tabbaci na dalilin da ya sanya wannan aika-aika ta afku, kasancewar mambobin jam'iyyar tuni sun gudanar da yarjejeniyar yadda aka shirya gudanar da taron jam'iyyar a yankin.

Shugaban jam'iyyar APC na Kasa; John Odigie-Oyegun

Shugaban jam'iyyar APC na Kasa; John Odigie-Oyegun

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, an samu tsaikon kayan aiki na gudanar da gangamin a kananan hukumomi daban-daban dake fadin jihar.

KARANTA KUMA: Mutane 10 sun ƙone ƙurmus a wani Hatsarin Tankar Mai a jihar Taraba

A na sa bangaren shugaban jam'iyya na jihar, Olorogun O'tega Emerhor, ya yabawa yadda aka gudanar da taron a mazabar sa ta Evwreni cikin lumana.

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa an gudanar da taron jam'iyyar cikin lumana a mazabu daban-daban dake kananan hukumomi 25 a fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel