2019: Ba na tunanin za a gudanar da zabe, Najeriya za ta tarwatse kafin lokacin - Adeboye

2019: Ba na tunanin za a gudanar da zabe, Najeriya za ta tarwatse kafin lokacin - Adeboye

A ranar Juma'ar da ta gabata ne babban limamin cocin Redeemed Christian, Fasto Enoch Adeboye, ya gargadi gwamnatin kasar nan da cewar ta yi gaggawar kawo karshen kashe-kashe a sassa daban-daban na kasar nan.

Babban Limamin ya yi gargadin cewa muddin aka ci gaba da zuba idanu kan halin da kasar nan take ciki na zubar da jini dan Adam ba tare da hakki ba to kuwa za a wayi gari ba bu ballantana labarin ta.

Fasto Adeboye ya yi wannan gargadi a yayin gudanar da harkokin su na ibada inda yake cewa muddin ba a kawo karshen kashe-kashe ba to ko shakka ba bu lallai zaben 2019 ya tabbata a kasar nan ta Najeriya.

Fasto Adeboye da Shugaba Buhari

Fasto Adeboye da Shugaba Buhari

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, babban limamin ya bayyana irin halin damuwa da suka shiga da iyalin sa a kasar Jamus yayin da suka samu rahoton makiyaya da suka kai hari wani coci a karamar hukumar Gwer ta jihar Benuwe.

KARANTA KUMA: Wata Mata ta tarwatsa 'ya'yan Marainan Makwabcin ta a jihar Legas

A yayin haka kuma babban limamin ya jagoranci mabiyansa wajen gudanar da addu'o'i da zasu warware matsalolin da kasar nan ke fama, inda ya ce duk da kasancewa kasar nan ta farfado bayan yakin basasa ba bu yadda za a yi hakan ya maimaitu muddin rikicin addini ya keto.

A sanandiya Fasto Adeboye ya ke mika kokon barar sa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya tashi tsaye wajen kawo karshen wannan rikici kafin ya sauya fasali zuwa na addini.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel