Fitataccen farfesa ya cacaki masu fakewa da rashin lafiya bayan an kama su da almundahana

Fitataccen farfesa ya cacaki masu fakewa da rashin lafiya bayan an kama su da almundahana

Shugaban kwamiti na musamman da ke bawa shugaban kasa shawara kan yaki da rashawa (PACAC), Farfesa Itse Sagay ya nuna takaicin sa kan yadda wasu 'yan Najeriya bige wa da rashin lafiya da zarar an fara binciken su game da wani laifi.

A wata hira da yayi da jaridar Daily Independent, Sagay ya ce abin kunya ne yadda mafi yawancin ma'aikatan gwamnati ke tsulla tsiyarsu cikin koshin lafiya amma da zaran an fara gudanar da binciken kasnsu sai su fara rashin lafiya na karya don mutane su tausaya musu.

Kalau suke lokacin da suke tafka tsiye amma da an cafke su sai su fara rashin lafiya - Sagay

Kalau suke lokacin da suke tafka tsiye amma da an cafke su sai su fara rashin lafiya - Sagay

KU KARANTA: A karo na farko, za'a gina wa Kiristoci coci a kasar Saudiyya

Da ya ke amsa tambayar da aka masa game da batun Sanata Dino Melaye da ya tafi kotu a gadon asibiti a ranar Alhamis, Sagay ya ce a halin yanzu ba zai iye tabbatar wa ko rashin lafiya Dino na gaskiya ne ba har sai asibiti ko kotu sun tabbatar da gaskiyar lamarin.

"Ina jin takaici kan yadda wasu masu rike da mukaman gwamnati ke labe wa da rashin lafiya duk lokacin da aka gurfanar da su a kotu. Daga abinda da nake gani a talabijin, ba zan iya tabbatarwa ko rashin lafiyar na gaskiya ne ko karya ba.

"A shari'ar Olisah Metuh, bisa ga dukkan alamu, kotun bata mayar da hankali kan rashin lafiyarsa ba. Kotun bata gamsu da cewa rashin lafiyar tayi tsanani kamar yadda yake kokarin nunawa ba. Dole ne muyi amfani da abinda kotu ta ce."

Sagay ya cigaba da cewa dama hakan mafi yawancin 'yan Najeriya keyi, za su rika aikata laifi cikin koshin lafiya da kuzari amma da an kama su, sai su bijiro da rashin lafiya sobada su kaucewa hukuncin laifin da sukayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel