Kashe-Kashe: Kungiyar Kiristoci sun shirya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga

Kashe-Kashe: Kungiyar Kiristoci sun shirya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga

Kungiyar kiristoci ta Najeriya baki daya ta sanar da kudurin ta na gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin su ga gwamnatin tarayyar Najeriya game da cigaban aukuwar hare-haren makiyaya a wuraren ibadar su ranar Lahadi mai zuwa.

Kamar dai yadda muka samu, kungiyar yanzu haka tana ta kara sanar da mabiya addinai a dukkan majami'un kasar nan da ma sauran masu fada aji da su fito kwansu-da-kwalkwata domin gudanar da zanga-zangar.

Kashe-Kashe: Kungiyar Kiristoci sun shirya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga

Kashe-Kashe: Kungiyar Kiristoci sun shirya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga

KU KARANTA: Buhari zai kaddamar da sabbin matatun mai a karshen shekarar nan

A wani labarin kuma, Wata hadakar kungiyoyin sa kai na al'ummar jihar Benue dake shiyyar arewa ta tsakiya da suka hada da Mdgzou U Tiv da na al'ummar Idoma da kuma na al'ummar Ngede sun sanar da samun nasarar kammala shire-shiren kai gwamnatin tarayya kara a majalisar dinkin duniya saboda kashe-kashen da ake yi wa al'ummar su yayi yawa.

Haka ma dai kungiyoyin sun bayyana cewa za su kai karar gwamnatin tarayyar dake karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a kotun kasa-da-kasa domin a bi masu hakkin su na diyya bisa abun da suka kila sakaci daga gwamnatin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel