Kashe-Kashe: Kungiyoyin sa kai sun shirya tsaf don kai karar Buhari majalisar dinkin duniya

Kashe-Kashe: Kungiyoyin sa kai sun shirya tsaf don kai karar Buhari majalisar dinkin duniya

Wata hadakar kungiyoyin sa kai na al'ummar jihar Benue dake shiyyar arewa ta tsakiya da suka hada da Mdgzou U Tiv da na al'ummar Idoma da kuma na al'ummar Ngede sun sanar da samun nasarar kammala shire-shiren kai gwamnatin tarayya kara a majalisar dinkin duniya saboda kashe-kashen da ake yi wa al'ummar su yayi yawa.

Haka ma dai kungiyoyin sun bayyana cewa za su kai karar gwamnatin tarayyar dake karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a kotun kasa-da-kasa domin a bi masu hakkin su na diyya bisa abun da suka kila sakaci daga gwamnatin.

Kashe-Kashe: Kungiyoyin sa kai sun shirya tsaf don kai karar Buhari majalisar dinkin duniya

Kashe-Kashe: Kungiyoyin sa kai sun shirya tsaf don kai karar Buhari majalisar dinkin duniya

KU KARANTA: An lalata bomabomai 15 a garin Enugu

Legit.ng ta samu cewa kungiyoyin dai daga karshe sun kuma roki dukkan hukumomin na duniya da idan sun kawo karar a yi mata karatun ta nutsu sannan a yi bincike sosai.

A wani labarin kuma, Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a matakin kasa baki daya a ranar Juma'ar da ta gabata ne dai ta kaddamar da wani muhimmin kwamitin da zai jagoranci kwace mulki daga hannun APC a zabukan 2019 masu zuwa.

Shuganan jam'iyyar na kasa ne dai Prince Uche Secondus ya kaddamar da kwamitin a babbar Sakatariyar jam'iyyar dake a garin Abuja yana mai cewa ya zama dole jam'iyyar ta kafa kwamitin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel