Hada-hadar miyagun kwayoyi: Najeriya za ta mikawa Amurka wani Sanata don yi masa hukunci

Hada-hadar miyagun kwayoyi: Najeriya za ta mikawa Amurka wani Sanata don yi masa hukunci

Wata kotun daukaka kara ta gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Legas ta yanke hukuncin cewa yanzu gwamnatin tarayya na da hurumin mika Sanata Buruji Kashamu dake wakiltar jihar Ogun ta gabas zuwa kasar Amurka bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi.

Wannan hukuncin da kotun ta yanke na matsayin yin fatali ne da wani hukunci da karamar kotu ta yanke game da batun na hana gwamnatin tarayyar ta kai shi.

Hada-hadar miyagun kwayoyi: Najeriya za ta mikawa Amurka wani Sanata don yi masa hukunci

Hada-hadar miyagun kwayoyi: Najeriya za ta mikawa Amurka wani Sanata don yi masa hukunci

KU KARANTA: Majalisar wakillai ta ayyana ranar zartar da kasafin kudin 2018

Legit.ng ta samu cewa alkalin kotun Mai shari'a Joseph Ikyeghi ya bayyana cewa a matsayin sa na dan kasa gwamnati na da ikon sa shi ya fuskanci shari'a a duk inda yake.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu da dumin sa daga kafofin yada labaran mu na nuni ne da cewa kwamitin da ke da alhakin gudanar da zabukan shugabannin jam'iyya mai mulki a jihar ta APC karkashin jagorancin Musa Mahmud ya dage yin zaben har sai zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

Musa Mahmud, kamar yadda muka samu ya sanar da hakan ne jim kadan bayan kammala tattaunawa da jiga-jigai da kuma masu ruwa da tsaki na jam'iyyar bisa dalilin cewar har yanzu akwai wasu da ba su samu damar sayen fom din su ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel