Mutane 10 sun ƙone ƙurmus a wani Hatsarin Tankar Mai a jihar Taraba

Mutane 10 sun ƙone ƙurmus a wani Hatsarin Tankar Mai a jihar Taraba

Kimanin rayuka goma ne suka salwanta yayin da wata tankar ta kama da wuta sakamakon wani mummunan hatsari tsakanin da wata babbar motar daukan kaya da ya afku a karamar hukumar Zing dake jihar Taraba.

Majiyar rahoton ta kuma bayyana cewa, kimanin mutane 20 sun samu raunuka daban-daban sakamakon hatsarin da ya afku a ranar Larabar da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan hatsari ya afku ne yayin da tankar makire da man fetur ke kan hanyar zuwa birnin Yola na jihar Adamawa ta afkawa wata babbar mota ta tirela.

Mutane 10 sun ƙone ƙurmus a wani Hatsarin Tankar Mai a jihar Taraba

Mutane 10 sun ƙone ƙurmus a wani Hatsarin Tankar Mai a jihar Taraba

Cikin kankanin lokaci tankar da kama balbalin wuta da ta lashe mutane da dama da suka hadar har da wata mata mai juna biyu.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya sauka a garin Daura domin halartar taron jam'iyyar APC a mazabar sa

A ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar 'yan sanda ta jihar ta tabbatar da afkuwar wannan hatsari da ya salwantar da rayukan mutane 10 nan take.

Kakakin hukumar, ASP David Missal ya bayyana cewa sauran mutane 20 da suka jikkata na samun kulawa a babban asibitin garin Zing da kuma cibiyar lafiya dake birnin Jalingo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel