Tangarɗar na'ura ce ta haifar da yanke albashin 'yan sanda na watan Afrilu- Kakakin Rundunar 'Yan Sanda

Tangarɗar na'ura ce ta haifar da yanke albashin 'yan sanda na watan Afrilu- Kakakin Rundunar 'Yan Sanda

- Ana gab da magance matsalar rashin biyan 'yan sanda albashinsu

- Ofishin Akanta Janar na kasa tare da Rundunar 'Yan sanda ne suka bayar da tabbacin jaka

Rundunar 'Yan Sanda ta Ƙasa ta danganta matsalar biyan albashin 'yan sanda na watan Afrilu ga tangarɗar na'ura.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, Jimoh Moshood ya bayar a Abuja ranar Juma'a, ya ce suna aiki tare da Ofishin Babban Akanta Janar na Ƙasa don warware matsalar biyan albashin.

Tangarɗar na'ura ce ta haifar da yanke albashin 'yan sanda na watan Afrilu- Kakakin Rundunar 'Yan Sanda

Tangarɗar na'ura ce ta haifar da yanke albashin 'yan sanda na watan Afrilu- Kakakin Rundunar 'Yan Sanda

A ta bakin Mista Moshood, Baban Akanta Janar na Ƙasa ya tabbatar da cewa waɗanda matsalar ta shafa za su sami cikon albashinsu kafin ko ranar 7 ga watan Mayu, 2018.

KU KARANTA: Dandadalin Kannywood: An gano masu rura wutar rikici tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango

Sanarwar ta ce: "Ofishin Babban Akanta Janar na Ƙasa ya tabbatar wa Rundunar 'Yan Sandar cewa matsalar biyan albashin da aka samu a watan Afrilun 2018 na 'yan sanda ta samu ne sakamakon tangarɗar na'ura kuma ana nan ana ƙoƙarin warware matsalar ba tare da jinkiri ba. Ana ci gaba da warware duk matsalolin da suke da dangantaka da albashin 'yan sanda".

A ta bakin Ofishin Babban Akanta Janar ɗin, waɗanda abin ya shafa za su sami cikon albashinsu kafin ko ranar Litinin, 7 ga watan Mayu, 2018.

Rundunar ta kuma bayyana cewa an buƙaci manyan jami'an 'yan sanda da su ilmantar da ma'aikatansu da suke da ƙorafi, tana mai ƙarawa da cewa kar su damu, domin kowa za'a biya shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel