Shugaba Buhari ya garzaya Daura domin halartan zaben jam’iyyar

Shugaba Buhari ya garzaya Daura domin halartan zaben jam’iyyar

Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga birnin tarayya Abuja zuwa kauyenshi da ke Daura, jihar Katsina domin kada kuri’arshi a zaben shugabannin jam’iyyan All Progressives Congress (APC) na gida.

Jam’iyyar ta sanya zaben ranan 5 ga watan Mayu domin gudanar da zabukan unguwanni, 12 ga Mayu na kananan hukumomi, da kuma 19 ga watan Mayu na jiha ga baki daya.

Shugaba Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Amurka ne da daren jiya Alhamis, 3 ga watan Mayu bayan ya yada zango kasar Landan.

Shugaba Buhari ya garzaya Daura domin halartan zaben jam’iyyar

Shugaba Buhari ya garzaya Daura domin halartan zaben jam’iyyar

Rashin dawowan shugaban kasan Najeriya bayan kwanaki biyu da barin Amurka ya tayar da hankulan jama’a. Amma bayan kafofin yada labarai sun wallafa wannan abin mamaki, mai Magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya yi fashin baki akan abinda yasa Buhari bai dawo ba.

KU KARANTA: Gaggan barayin mutane tare da yan fashi da makami su 6 sun fada tarkon Yansanda a jihar Katsina

Garba Shehu ya bayyana cewa n dakatad da zuwan shugaba Buhari ne saboda karamar jirgi ya hau kuma ba zata iya dogon tafiya ba.

Yace jirgin da shugaban kasan yayi amfani da shi awanni 12 da minti 40 kawai zai iya yi kuma tafiyar Amurka zuwa Najeriya awa 12.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel