An gano wata makarkashiya ta kashe shugabar kasar Birtaniya

An gano wata makarkashiya ta kashe shugabar kasar Birtaniya

- Naa’imur Rahman dan ta'adda ne da ya amsa laifinsa na kokarin kisan kai

- Yaso ya fasa bam ne a inda Firai Ministar take taro a Landan

- Ya taimaka wa wasu shiga kungiyar jihadin Islama ta IS

An gano wata makarkashiya ta kashe shugabar kasar Birtaniya

An gano wata makarkashiya ta kashe shugabar kasar Birtaniya

Naa’imur Rahman wani saurayi ne da aka kama da bama-bamai yana kokarin tayar dasu a harabar fadar gwamnatin Birtaniya ta Downing Street a birnin Landan, da niyyar kashe jama'a sannan ya shiga hargitsin domin kisan shugaba May.

Tun a watan Nuwamba aka kamo shi, amma yaki amsa laifukan da ake zarginsa dasu bayan da aka kaishi kotu. Ya kuma ki amsa cewa shi dan kungiyar IS ne.

DUBA WANNAN: Ashe N100 aka barnatar kan takurawa Dino Melaye

Ya bayar da shaidar yadda yake dauko wa 'yan kungiyar ta IS ma'aikata da mayaka a fadin yankin Turai.

Gwamnatin ta Birtaniya kuma, ta zarge shi da kokarin zuwa kasar Libiya domin karo ilimin tayar da bama-bamai da harbi domin dawowa yayi mugun aikinsa a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel