Da duminsa: Alkalin Alkalan jihar Kogi ya bayar da umurnin mayar da Dino Melaye zuwa Abuja

Da duminsa: Alkalin Alkalan jihar Kogi ya bayar da umurnin mayar da Dino Melaye zuwa Abuja

Alkalin Alkalai na Jihar Kogi, Nasir Ajanah ya bayar da izinin mayar da Sanata Dino Melaye zuwa asibitin kasa da ke babban birnin tarayya Abuja saboda ya samu ingantaccen kulawa.

Ajanah ya bayar da umurnin ne a yau Juma'a a garin Lokoja, inda ya kara da cewa za'a saurari shari'ar neman bayar da belin Dino Melaye a ranar Litinin.

Alkalin Alkalan yace ya bayar da umurnin ne saboda asibitin kurkukun da ake tsare Dino Melaye ba ta da isasun kayan aikin da za'a kula da lafiyar Sanatan.

Da duminsa: Alkalin Alkalan jihar Kogi ya bayar da umurnin mayar da Dino Melaye zuwa Abuja

Da duminsa: Alkalin Alkalan jihar Kogi ya bayar da umurnin mayar da Dino Melaye zuwa Abuja

KU KARANTA: Kungiyar musulmi ta JNI ta bukaci jama'a su farga saboda jami'an tsaro sunyi sanyi

Ya furta hakan ne lokacin da Mike Ozekhome, lauya mai kare Dino Melaye ya shigar da takardan neman beli.

Ana tuhumar Dino Melaye ne da laifukan da suka hada da makirci da kuma sayan makamai wanda ya bawa wasu yan bindiga. Wata kotun majistare ta hana shi beli inda kotun tace yan sanda su cigaba da tsare shi har zuwa ranar 11 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel