Atiku ya yabawa Hukumar INEC kan batun mahawara a tsakanin 'Yan Takara

Atiku ya yabawa Hukumar INEC kan batun mahawara a tsakanin 'Yan Takara

Tsohon shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya yi martani ga kiran hukumar INEC na muhawara a tsakanin 'yan takara masu neman kujeru a kasar nan a zaben 2019.

Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon shugaban kasa ba ya da wata fargaba akan gudanar da muhawara inda yake yabawa hukumar INEC dangane da wannan kira da ta yi.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban hukumar zabe na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, cikin wata sanarwa yayin taron kafofin watsa labarai a birnin Legas da aka gudanar ya yi wannan kira na muhawara tsakanin 'yan takara a kasar nan.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa, muhawara a tsakanin 'yan takara na da matukar muhimmanci cikin tsarin dimokuradiyya da za ta tallafa wajen jagorantar masu kada kuri'u wajen zaben fitacce a cikin su.

KARANTA KUMA: Sanata Shehu Sani ya goyi bayan Shugaba Buhari akan batun 'Yan Sandan Jiha

A yayin haka ne tsohon shugaban kasar cikin wani sako da ya rubuta a shafin sa na sasa zumunta ya bayyana cewa, ya na matukar murna gami da yabawa hukumar INEC dangane da wannan kira da ta aiwatar da zai taka rawar gani cikin tsarin dimokuradiyya.

Ya kara da cewa, tsarin shugabanic na dimokuradiyya a kasar nan zai ingantu ta hanyar bayar da dama ga masu kada kuri'in zaben wajen tantance managarcin shugaba kafin su zabe shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel