Majalisar dattijai na bincikar yadda biliyoyin kudaden fanshon sojoji suka bace bat

Majalisar dattijai na bincikar yadda biliyoyin kudaden fanshon sojoji suka bace bat

- Ana cin zalin kananan kuratan sojoji a NAjetiya

- Su kuma sojin su ke yaki a dazuka, sun kuma fi mutuwa a filin daga

- Manyan soji ke wawure fanshonsu su boye domin kudin ruwa

Majalisar dattijai na bincikar yadda biliyoyin kudaden fanshon sojoji suka bace bat

Majalisar dattijai na bincikar yadda biliyoyin kudaden fanshon sojoji suka bace bat

Binciken majalisar Dattijai na wawure kudaden kananan sojoji na fansho ya nuna cewa akalla N44b ne a tsakanin shekarun 2013-2017 basu isa ga masu hakki ba inda aka canja akalar kudaden zuwa wasu asusun don neman riba.

A bayanan na baya-bayan nan, Ministar Kudi Adeosun, tace an kuma gano wasu biliyan kusan biyu a wani assusun suna bacci babu mai-su a wani babban bankin 'yan kasuwa, bayan da aka tattaro kudaden aka kaisu asusun bai-daya na TSA.

DUBA WANNAN: Anyi min wahayi Buhari ba zai zarce ba

Asusun na ansho, ya amshi N13.5 billion a 2015, N16.6 billion a 2016 da N15. 422 billion a 2017, inji ofishin Akanta Janar na kasa nan.

Kwamitin ya baiwa hukumar zuwa talata da su fitar masa da dukkan takardu da bayanai da ake bukata don aga inda kudaden suka makale, ko kuma wa ya handame su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel