Ministan Buhari ya kalubalanci masu labarai akan rahoton adalci

Ministan Buhari ya kalubalanci masu labarai akan rahoton adalci

- Ministan sadarwa da al’adu,Alhaji Lai Mohammed ya kalubalanci masu labarai dasu kasance masu adalci a wurin labaran da suke bayarwa game da gwamnati

- Ministan yayi kalubalan ne a jawabinsa na ranar ‘yancin manema labarai na shekarar 2018, wanda aka yiwa take da ‘Keeping Power in Check: Media, Justice and Rule of Law’

- Ministan yace babbar garkuwar siyasa itace ta manema labarai, saboda sune kadai zasu iya kalubalantar ko wanene a kowane matsayi yake na gwamnati

Ministan sadarwa da al’adu,Alhaji Lai Mohammed ya kalubalanci masu labarai dasu kasance masu adalci a wurin labaran da suke bayarwa game da gwamnati.

Ministan yayi kalubalan ne a jawabinsa na ranar ‘yancin manema labarai na shekarar 2018, wanda aka yiwa take da “Keeping Power in Check: Media, Justice and Rule of Law”, a birnin tarayya a jiya.

Ministan Buhari ya kalubalanci masu labarai akan rahoton adalci

Ministan Buhari ya kalubalanci masu labarai akan rahoton adalci

Ministan yace babbar garkuwar siyasa itace ta manema labarai, saboda sune kadai zasu iya kalubalantar ko wanene a kowane matsayi yake na gwamnati game da abunda yayi.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta (hoto)

Lokacin da yake jawabi game da kokarin manema labarai da irin rawar gani da suka taka a fannin cigaban siyasar Najeriya, Alhaji Lai Mohammed yace ya kamata manema labarai su kara bunkasa aikinsu gaba al’amuran siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel