Hukumar INEC tace makafi zasu kada kuri'a ta hanyar amfani na'urar Braille

Hukumar INEC tace makafi zasu kada kuri'a ta hanyar amfani na'urar Braille

Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC tace zata samarwa makafi masu shekaru 18 da sama da haka wata na'urar na musamman mai suna Braille domin su sami damar kada kuri'a a zaben 2019.

Hukumar ta kara da cewa za ta tabbatar da cewa duk wani mutum da yake da wata nakasa ya samu damar kada kuri'ar sa kamar yadda sauran mutane za suyi a zaben na 2019.

Shugaban hukumar INEC Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wani taro da suka gudanar dangane da ci gaba da yin rijistar zabe a jami'ar Abuja ranar Alhamis.

Hukumar INEC tace makafi zasu kada kuri'a ta hanyar amfani na'urar Braille

Hukumar INEC tace makafi zasu kada kuri'a ta hanyar amfani na'urar Braille

Shugaban ya bayar da wannan amsar ne a yayin da wani makahon mai shirye wakoki, Cobhams Asuquo , ya roki shi da ya taimakawa wa mutane masu nakasa don su samu damar kada kuri'ar nasu a cikin sirri ba tare da wani ya taimaka musu ba.

KU KARANTA: An sallami Farfesa da wani malami daga Jami'ar ATBU ta Bauchi

Shugaban INEC yace a yayin zaben gwamna a Anambra sun samar wa duk wani zabiya gilashi mai kara karfin idanu don ya sami damar kada kuri'a sannan yayin da kuma yayi alkawarin kawo kujeru ga garagu.

Yakubu yace "don samun ci gaba zamu samar da na'urar braille saboda makafi, sannan mun riga mun samarwa zabiyoyi gilashi, guragu kuwa zamuyi kokarin samar musu da kujerun guragu."

Ya bayyana wa dalibai cewa an bude musu wajen yin rijista a cikin makarantu sannan ya shawarce su yi amfani da damar da suka samu.

Sannan yace duk wanda yayi rigista a 2017 yaje ya karbi katin zaben sa na din din din.

Da yake bawa wani dalibi amsar tambayar da yayi akan cewa yayi rijista katin zabe tun yana da shekaru 12 yace hakan ya sabawa doka dan shekaru 18 ne kadai aka yarje masa kada kuri'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel