‘Yan kunar bakin wake sun sake kai hari a garin Maiduguri

‘Yan kunar bakin wake sun sake kai hari a garin Maiduguri

- ‘Yan kunar bakin wake hudu sun kai hari a kauyen Mairanti dake kusada garin Maiduguri a ranar Alhamis

- Anji karar tashin bam da misalin karfe 10 na dare lokacin da yawanci mutane na cikin gidajensu, amma dai anyi sa’a ba’ayi asarar rayuka ba sai masu kunar bakin waken

- Kungiyar masu bayar da taimakon gaggawa NEMA Bashir Garba yace akwai yiwuwar masu kunar bakin waken suna yawan shigowa kauyen saboda haka yake jan kunnen ‘yan kauyen dasu kaa kulawa

‘Yan kunar bakin wake hudu sun kai hari a kauyen Mairanti dake kusada garin Maiduguri a ranar Alhamis

Anji karar tashin bam da misalin karfe 10 na dare lokacin da yawanci mutane na cikin gidajensu, amma dai anyi sa’a ba’ayi asarar rayuka ba sai masu kunar bakin waken

Kungiyar masu bayar da taimakon gaggawa NEMA Bashir Garba yace akwai yiwuwar masu kunar bakin waken suna yawan shigowa kauyen saboda haka yake jan kunnen ‘yan kauyen dasu kaa kulawa, bayan ya tabbatarwa gidan Talabijin na Chennels da aukuwar lamarin.

‘Yan kunar bakin wake sun sake kai hari a garin Maiduguri

‘Yan kunar bakin wake sun sake kai hari a garin Maiduguri

Miranti wadda ke kusada Molai a kan hanyar babban birnin jihar, ta kasance wurinda ake yawan kaiwa hari a ‘yan kwanakinnan.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta (hoto) 'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta (hoto)

A watan Afirilu mutane tara aka kashe wadanda suka hada da jami’an ‘Yan Sanda biyu da suka samu raunuka sakamakon wadanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari a Jiddari Polo dake Maiduguri, a jihar Borno.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel