Allah ya fada mani cewa Buhari zai bar mulki a 2019 sannan ni na cigaba – Babban malami yayi hasashe

Allah ya fada mani cewa Buhari zai bar mulki a 2019 sannan ni na cigaba – Babban malami yayi hasashe

- Malamin kirista, Fasto Gabriel Adegboye, ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasar Najeriya na gaba, bayan ya bayyana cewa Ubangiji ya bayyana masa cewa wa’adin shugaba Buhari zai kar a shekaru hudu

- Adegboye tare da wasu mambobinsa na kungiyar ‘Save Najeriya 2019 Movement’ ya bayyanawa manema labarai cewa ya samu wahayin magance matsalolin Najeriya

- Adegboye yace kungiyar tasu tana sasantawa da jam’iyyun Najeriya kuma zata shiga jam’iyyar data amince da al’amurransa

Malamin kirista, Fasto Gabriel Adegboye, ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasar Najeriya na gaba, bayan ya bayyana cewa Ubangiji ya bayyana masa cewa wa’adin shugaba Buhari zai kar a shekaru hudu.

Adegboye tare da wasu mambobinsa na kungiyar ‘Save Najeriya 2019 Movement’ ya bayyanawa manema labarai a garin Ibadan, cewa ya samu wahayin magance rikici da kuma kisan da akeyi a arewa maso gabashi da kuma sauran wuraren dake fadin Najeriya tare da tabbatar da cigaban tattalin arzikin kasar.

Kamar yadda ya bayyana rikicin Boko Haram a matsayin wani asiri da aka yiwa kasar daga arewacin Afirika, inda Adegboye ya bayyan cewa yana da hanyar magance wannan matsalar cikin watanni uku.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta (hoto)

Adegboye yace kungiyar tasu tana sasantawa da jam’iyyun Najeriya kuma zata shiga jam’iyyar data amince da al’amurransa.

Adegboye kuma ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta INEC data rage kudin takardar shiga cikin wadanda hukumar ta amince suyi takara a zaben, saboda a kara samun yawan wadanda keda sha’awar tsayawa takarar ta shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel