Za mu sake duba farashin wutar lantarki - Hukumar kula da wuta, NERC

Za mu sake duba farashin wutar lantarki - Hukumar kula da wuta, NERC

Hukumar nan mallakin gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da harkokin samar da wutar lantarki ga al'ummar kasa watau Nigerian Electricity Regulatory Commission, NERC a takaice ta bayyana kudurin ta na sake yin bitar farashin wutar da al'umma ke tu'ammali.

Wannan tabbacin dai ya fito ne daga bakin sabon shugaban hukumar Farfesa Jame Momoh inda kuma ya ayyana cewa tuni shirye-shirye domin yin hakan sun kankama a dukkan fadin kasar.

Za mu sake duba farashin wutar lantarki - Hukumar kula da wuta, NERC

Za mu sake duba farashin wutar lantarki - Hukumar kula da wuta, NERC

KU KARANTA: Sa'adiya Gyale ta ce za ta iya dawowa fim

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Farfesa James ya kuma kara jaddada kudurin gwamnatin tarayya karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari na samar da wutar lantarki a mafi karancin kudi domin al'umma.

A wani labarin kuma, Majalisar wakilai a tarayyar Najeriya ta ayyana cewa ta kammala shire-shiren zartas da kasafin kudin shekarar 2018 a matsayin doka a cikin sati mai kamawa kamar dai yada Honorable Abdulrazaq Namdas da ke zaman mai magana da yawun majalisar ya fadawa manema labarai a jiya.

A cewar Abdulrazaq Namdas 'yan majalisar sun dauki kasafin kudin da muhimmacin gaske shi ya sa ma suka hanzarta kammala aiki kan sa kuma suke shirin kai shi a zauren ranar Talata mai zuwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel