Kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya gidaje 2 da Naira milliyan 11 na manyan sojojin ruwan Najeriya

Kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya gidaje 2 da Naira milliyan 11 na manyan sojojin ruwan Najeriya

Wata kotun gwamnatin tarayya da ke zaman ta a garin Legas a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayar da da umurnin mallakawa gwamnatin tarayya wasu manyan gidajen alfarma guda biyu mallakin wasu manyan jami'an sojin ruwan Najeriya Kaftin Olotu Morakinyo da kuma Kaftin Ebony Aneke.

Alkalin kotun, mai shari'a Muslim Hassan shine ya yanke wannan hukuncin biyo bayan karar da hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta shigar a gaban sa.

Kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya gidaje 2 da Naira milliyan 11 na manyan sojojin ruwan Najeriya

Kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya gidaje 2 da Naira milliyan 11 na manyan sojojin ruwan Najeriya

KU KARANTA: Za mu tabbata Fayose yaje gidan yari - Fayemi

Legit.ng ta samu haka zalika cewa kotun ta kuma mallakawa gwamnatin tarayyar makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 11 da ake kyautata zaton mallkakar Kaftin Aneke ne.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya ya kara jaddada matsayar sa ta cewa tabbas shugabannin kasar Najeriya da suka shude ne musabbabin lalacewar Najeriya duba da yadda ya ce sun mulki kasar.

Haka zalika shugaban kasar wanda mataimakin sa ya wakilta a wajen taron karawa juna ilimi da likitocin Najeriya suka shirya, ya kuma dora alhakin tabarbarewar fannin harkar lafiya kacokan a kan gwamnatin da ta shude ta shugaba Jonathan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel