NDPHC: Majalisa ta bayar da umurnin mayar da Maryam Danna bakin aikinta

NDPHC: Majalisa ta bayar da umurnin mayar da Maryam Danna bakin aikinta

- A jiya ne majalisa ta bayar da umurnin gaggauta mayar da Janar Manaja (Audit and Compliance) ta kamfaninwutar lantarki (NDPHC) dake Niger Delta, Mrs Maryam Danna Mohammed

- Shawarar majalisar tazo ne bayan watanni 19 da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin cewa a mayar da Maryam Mohammed wadda aka kora daga aiki a watan Yuni na 2016, bakin aiki

- Shawarar tazo ne bayan la’akari da rahoton kwamitin majalisar da suka gabatar game da korafin Mrs Mohammed wanda Sanata Baba kaka Bashir Garbai ya gabatar na APC Borno

A jiya ne majalisa ta bayar da umurnin gaggauta mayar da Janar Manaja (Audit and Compliance) ta kamfaninwutar lantarki (NDPHC) dake Niger Delta, Mrs Maryam Danna Mohammed.

Shawarar majalisar tazo ne bayan watanni 19 da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin cewa a mayar da Maryam Mohammed wadda aka kora daga aiki a watan Yuni na 2016, bakin aiki.

Shawarar tazo ne bayan la’akari da rahoton kwamitin majalisar da suka gabatar game da korafin Mrs Mohammed wanda Sanata Baba kaka Bashir Garbai ya gabatar na APC Borno.

NDPHC: Majalisa ta bayar da umurnin mayar da Maryam Danna bakin aikinta

NDPHC: Majalisa ta bayar da umurnin mayar da Maryam Danna bakin aikinta

Bayan mayar da ita bakin aiki majalisar ta umurci kamfanin na NDPHC da ya biya Mrs Mohammed duk kudaden daya kamata, sannan kuma korar da akayi mata an bi ka’idojin da suka kamata na mayar da ita.

KU KARANTA KUMA: Dalilan da ya sa jaruman Arewa ba za su iya fitowa a shirin ‘Big Brother’ ba – Fati SU

Shugaban kwamitin Sam Anyanwu (PDP, Imo) yace matsayin da aka bawa Mrs Mohammed a matsayi Janar Manaja (Audit and Compliance) a kamfanin na NDPHC ba kawai nadata akayi ba, cancanta ce tasa aka nadata a matsayinta na ma’aikaciyar kamfanin wadda ta biyo ta hanyarmatakan da suka kamata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel