APC za ta gudanar da zaben Shugabannin Jam’iyya a gobe

APC za ta gudanar da zaben Shugabannin Jam’iyya a gobe

- APC za ta yi zaben Shugabannin ta na kananan Hukumomi gobe

- ‘Yan Majalisu sun tattara sun bar Abuja domin ganin an yi da su

- Ana zargin cewa Gwamnoni na kokarin nuna karfin iko a zaben

Jam’iyyar APC za ta gudanar da zaben ‘Ya ‘yan ta a Mazabu da Yankunan kasar nan a gobe. A Ranar Asabar dinnan ne Shugabannin kananun Hukumomin Jam’iyyar sama da 9500 za su bayyana.

APC za ta gudanar da zaben Shugabannin Jam’iyya a gobe

Jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben kananan Hukumomi

A gobe 5 ga Watan Mayu nan ne aka shirya gudanar da zaben Shugabannin Jam’iyyar APC a Kananan Hukumomi 774 na Jihohi 36 da ake da su a Najeriya. Tuni dai ‘Yan Majalisun APC sun bar Birnin Tarayya domin shriyawa zaben gadan-gadan.

KU KARANTA: Sanatoci na daf da bankado wata badakala a Gwamnatin Buhari

Labarin da mu ke samu daga Jaridar Daily Trust shi ne ‘Yan Majalisun Tarayya na Jam’iyyar APC sun koma Kauyukan su domin su kara da Gwamnonin Jihohi a wajen zaben. Ana dai zargin cewa Gwamnonin na kokarin kakaba mutanen su.

Bayan an yi wannan zaben ne kuma za a zo a zabi Shugabannin Jam’iyyar na Jihohi. Daga nan kuma za a zabi Shugabannin Jam’iyyar ta APC da za su rike kasar. Zaben Jihohin da za ayi zai biyo baya ne a makon gaba Inji wani Jami'in Jam’iyyar.

Bolaji Abdullahi wanda shi ne Sakataren yada labarai na Jam’iyyar yace a watan Yuni za ayi zaben kasa. Sai dai kun ji cewa har yanzu Jam’iyyar ba ta sa ranar da za ayi zaben ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel