Sama da mutane 100 suka rasa rayukansu a guguwar kasa da akayi a kasar Indiya

Sama da mutane 100 suka rasa rayukansu a guguwar kasa da akayi a kasar Indiya

- A kalla mutane 109 suka rasa rayukansu sannan da dama sun samu raunuka a guguwar kasa data shafi jihohin arewacin Indiya na Uttar Pradesh da Rajasthan

- Guguwar wadda ta auku a ranar Laraba ta lalata wutar lantarki, ta cire itace, ta kuma lalata gidaje sannan ta kashe dabbobin gida

- Dayawa cikin wadanda suka rasu abun ya samesu ne suna cikin bacci lokacin da guguwar ta taso sakamakon walkiya mai karfi

A kalla mutane 109 suka rasa rayukansu sannan da dama sun samu raunuka a guguwar kasa data shafi jihohin arewacin Indiya na Uttar Pradesh da Rajasthan.

Guguwar wadda ta auku a ranar Laraba ta lalata wutar lantarki, ta cire itace, ta kuma lalata gidaje sannan ta kashe dabbobin gida.

Guguwar kasar ba sabon abu bane wadannan yankun na kasar Indiya lokacin rani, amma yawan rayukan da aka rasa a wannan karon da guguwar ta taso abun mamaki ne.

Dayawa cikin wadanda suka rasu abun ya samesu ne suna cikin bacci lokacin da guguwar ta taso sakamakon walkiya mai karfi.

Sama da mutane 100 suka rasa rayukansu a guguwar kasa da akayi a kasar Indiya

Sama da mutane 100 suka rasa rayukansu a guguwar kasa da akayi a kasar Indiya

A kalla mutane 73 sika mutu a Uttar Pradesh, kuma fiye da rabinsu daga kauyen Agra wanda nanne asalin gida ga Taj Mahal Monument, jami’ai sunce yawan rayukan da aka rasa zai iya karuwa.

KU KARANTA KUMA: Dalilai 5 da suka haddasa wa Obasanjo kiyayya ga Buhari

Jami’in labarai Laxmikant Pachouri ya fadawa BBC cewa mutane 21 suka rasu a kauyen Kheragarh, wanda ke nisan 50km (30 miles) na kudu maso yammacin Agra.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel