Asirin wani kwarto da ya je yin fyade ga tsohuwa mai shekaru 110 ya tonu

Asirin wani kwarto da ya je yin fyade ga tsohuwa mai shekaru 110 ya tonu

- Kwamacala kenan, jami'an tsaro sunyi ram da wani kasurgumin kwarto

- Kuma yanzu haka yana can gida Maza garkame, bayanda aka damke shi

Kotu ta ingiza keyar wani kwarto dan shekara 56 gidan kurkuku bayan da yan sanda suka gurfanar da shi bisa zargin nufin haikewa wata tsohuwa mai shekaru 110.

Asirin wani kwarto da ya je yin fyade ga tsohuwa mai shekaru 110 ya tonu

Asirin wani kwarto da ya je yin fyade ga tsohuwa mai shekaru 110 ya tonu

Dan sanda mai gabatar da kara sufeto Insp. Caleb Leranmo, ya shaidawa kotun cewa, sun kama mutumin ne ranar 30 ga watan Afrilu, yayin da ya afka gidan gyatumar dake gida mai lamba 12 a layin Igbehin a garin Ado Ekiti. A cewarsa, wannan laifi ne da ya saba da sashi na 359 na kudin manyan laifuka (2012) na jihar ta Ekiti.

KU KARANTA: Gaggan barayin mutane tare da yan fashi da makami su 6 sun fada tarkon Yansanda a jihar Katsina

Bayan sauraron karar ne, mai shari'a Taiwo Ajibade, ya bayar da umarnin tafiya da shi gidan yari kafin ranar 22 ga watan Mayu domin cigaba da shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel