Limaman Addini za su tada zaune tsaye idan aka cigaba da kashe jama'a

Limaman Addini za su tada zaune tsaye idan aka cigaba da kashe jama'a

- Pentacostal Fellowship of Najeriya PFN sunyi barazanar daukar matakin gagarumar zanga-zanga nan da wata daya idan har gwamnatin tarayya ta gaza tsayar da kisan kiristoci a yankin tsakiya da kuma sauran yankunan Najeriya

- Mataimakin shugaban kungiyar ta PFN Bishop Simeon Okah, yayi maganganu game da kisan da akeyi a fadin kasar nan a cikin shekaru uku da suka gabata

- Okah ya bayyana cewa wadanda aka kashe a yankin tsakiyar Najeriya yawanci kiristoci ne, saboda suna kokarin ganin cewa duk wanda ke kiran Yesu a cikin addininsa an kawar dashi

Pentacostal Fellowship of Najeriya PFN sunyi barazanar daukar matakin gagarumar zanga-zanga nan da wata daya idan har gwamnatin tarayya ta gaza tsayar da kisan kiristoci a yankin tsakiya da kuma sauran yankunan Najeriya.

Mataimakin shugaban kungiyar ta PFN Bishop Simeon Okah, yayi maganganu game da kisan da akeyi a fadin kasar nan a cikin shekaru uku da suka gabata, cewa sunfi yawan wadanda aka kashe tun bullowar kungiyar ‘Yan Boko Haram.

Okah ya bayyana cewa wadanda aka kashe a yankin tsakiyar Najeriya yawanci kiristoci ne, yace saboda; “suna kokarin ganin cewa duk wanda ke kiran Yesu a cikin addininsa an kawar dashi kuma ina iya baka shiada akan hakan. Banda yankin tsakiyar Najeriya mun san ana kashe mutane a fadin kasar nan.

KU KARANTA KUMA: APC, PDP bazasu iya kai Najeriya inda take mafarkin zuwa ba – Shehu Sani

“Ana kashe mutane tun kafin shugaba Muhammadu Buhari ya karba mulki, amma zaka amince da cewa yawan kisan da akayi a cikin shekaru uku da suka gabata idan aka hadasu baki daya, ya wuce yawan kisan da ‘yan kungiyar Boko Haram sukayi tun lokacin bullowar kungiyar."

Idan bazaku manta ba a kwanan nan ne muka ji cewan an kashe wasu fastoci biyu da masu bauta 17 a wani coci dake jihar Benue.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel