'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta (hoto)

'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta (hoto)

- Dalibai hudu na makarantar Whitesands, Lekki sun zamo zakaru a gasar Conrad Foundation Spirit of Innovation

- Daliban sune Afolabi Wiliiams, Olubusiyi Famobiwo, Menashi Mordi da kuma Osagumwenro Naaman Ugbo, sune suka zamo zakarun duniya na gasar Smoke-Free

- Daliban da suka gudanar da gasar mai lakabin Smoke-Free Challenge sun yita ne akan samarwa manoman taba mafita gameda matsalar hayakin tabar

Dalibai hudu na makarantar Whitesands, Lekki sun zamo zakaru a gasar Conrad Foundation Spirit of Innovation.

Daliban sune Afolabi Wiliiams, Olubusiyi Famobiwo, Menashi Mordi da kuma Osagumwenro Naaman Ugbo, sune suka zamo zakarun duniya na gasar Smoke-Free, wadda aka gudanar a Kennedy Space Center Visitor Complex, a garin Florida dake kasar Amurka.

'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta

'Yan Makarantan Najeriya sun je har Amurka sun ciri tuta

Daliban da suka gudanar da gasar mai lakabin Smoke-Free Challenge sun yita ne akan samarwa manoman taba mafita gameda matsalar hayakin tabar, musamman a kasashen dake tasowa ta fannin cigaba.

KU KARANTA KUMA: APC, PDP bazasu iya kai Najeriya inda take mafarkin zuwa ba – Shehu Sani

Sune kadai wadanda suka wakilci Najeriya da kuma Afirika a fagen gasar nan karshe. Daliban sun samu kyautar KSCVC ta ‘yan kasa na gari a wurin gasar.

Malamin ICT Methew Omotoso, na makarantar ta Whitesands shine ya raka daliban, wanda kuma bankin Guaranty Trust Bank shine ya dauki nauyin tafiyar tasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel