Sanata Shehu Sani ya goyi bayan Shugaba Buhari akan batun 'Yan Sandan Jiha

Sanata Shehu Sani ya goyi bayan Shugaba Buhari akan batun 'Yan Sandan Jiha

Sanata mai wakiltar Jihar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya kan batun rashin amincewa da samar da 'yan sandan jihohi a kasar nan kamar yadda gwamnoni suka bukata.

A kwanan-kwanan shugaba Buhari cikin wata ganawa da kafar watsa labarai ta Muryar Amurka, ya sake jaddada matsayar sa kan batun samar da 'yan sandan jiha da cewar har yanzu ba bu wata hujja da hakan zai taimaka wajen kawar da kalubalen tsaro da kasar nan ke fama.

Sanata Shehu Sani ya goyi bayan Shugaba Buhari akan batun 'Yan Sandan Jiha

Sanata Shehu Sani ya goyi bayan Shugaba Buhari akan batun 'Yan Sandan Jiha

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin ciwon baki da takaici babban dalili guda da shugaba Buhari ya bayar shine ba zai yiwu a baiwa ma'aikata makamai ba kuma su shafe tsawon watanni ba tare da albashi ba kamar yadda wasu gwamnoni ke yi a kasar nan.

KARANTA KUMA: Kuri'un 'Yan Najeriya su za su tantance sakamakon Zaben 2019 - INEC

A yayin mara baya ga shugaba Buhari, Sanatan a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cikin wani sako a shafin sa na sada zumunta cewa, samar da 'yan sandan jihohi zai bayar da dama ga wasu gwamnoni su yi amfani da 'yan ta'adda sanya cikin kayan jami'ai kuma rike da makamai wajen biyan bukatun su.

A sanadiyar haka ne Sanatan yake yabawa shugaba Buhari dangane da matsayar sa ta rashin amincewa da samar da 'yan sandan jiha, inda yake cewa yiwuwar hakan zai baiwa wasu gwamnoni dama ta tafka ta'asa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel