Gwamnan jihar Kaduna ya karbi bakoncin Babban kwamandan Sojojin runduna ta 1

Gwamnan jihar Kaduna ya karbi bakoncin Babban kwamandan Sojojin runduna ta 1

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya karbi bakon babban kwamandan runduna ta daya na Sojojin kasa, Manjo Janar Muhammad Muhammad a ranar Alhamis, 3 ga watan Mayu na shekarar 2018.

Muhammad ya ishe gwamnan ne a fadar Gwamnatin jihar, gidan Sir Kashim Ibarahim, tare da rakiyar wasu manyan hafsoshin Soji dake aiki a runduna ta daya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Kaico! Injin surfe ya hallaka wata Uwargida a babban birnin tarayya Abuja

Gwamnan jihar Kaduna ya karbi bakoncin Babban kwamandan Sojojin runduna ta 1

Ziyarar

Tsohon Kaakakin rundunar Sojin kasa, Birgediya SK Usman ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook, inda ya daura hotunan Kwamandan da gwamnan tare da manyan hadiman gwamnatin jihar, duk a yayin ziyarar.

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kaduna,Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana tsaro a matsayin ginshikin duk wani cigaba da bukatar samu, inda yace babu abinda zai yiwu a inda babu ingantaccen tsaro.

Gwamnan jihar Kaduna ya karbi bakoncin Babban kwamandan Sojojin runduna ta 1

Ziyarar

El-Rufai ya bayyana haka ne a yayin ganawa da daliban kwas na 40 na kwalejin horas da manyan jami’an gwamnati, dake Kuru, Jos, jihar Filato, a lokacin da suka kai masa ziyara a fadar gwamnati, tare da gudanar da bincike kan karfafa tsaro a Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna ya karbi bakoncin Babban kwamandan Sojojin runduna ta 1

Ziyarar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel