Dalilan da ya sa jaruman Arewa ba za su iya fitowa a shirin ‘Big Brother’ ba – Fati SU

Dalilan da ya sa jaruman Arewa ba za su iya fitowa a shirin ‘Big Brother’ ba – Fati SU

Shahararriyar jaruman nan ta Kannywood, Fati SU ta bayyana dalilan da yasa yasa jarumai irin su da wasu shahararru a fannin nishadantarwa dake Arewacin Najeriya ba za su iya fitowa a shirin ‘Big Brother’ ba.

A cewarta hakan ya samo asali ne ganin yadda yayi karo da dabi’un mutanen yankin ba da addinin musulunci.

Fati ta kara da cewa babu shakka za ta so ta kasance a cikin wannan shiri ko dan saboda kyaututtuka da kudaden da ake ci amma sai dai hakan ba zai samu ba saboda ya saba wa kyarwar adininta da al’adun yankin.

Tace: "Fitowa a irin wadannan shiri ga mutane irin mu (‘Yan Arewa) ya matukar saba wa adinin mu da al’adanmu a Arewa.

“Misali abubuwan da ‘yan wasan ke yi ya saba wa koyarwar addini na da al’adata kamar sumbatar juna da skey karara, rungumar juna, yadda suke saka kaya suna nuna tsiraicin su baro-baro kuma a nuna a talabijin duniya ta gani. Sannan koda mutum ya yi taurin kai ya shiga cikin shirin, ba karamin suka zai samu ba.

KU KARANTA KUMA: Matasa a Arewa na shirin gudanar da zaben sobin-tabi ga masu takara

“Ku tuna abunda ya faru da Rahama Sadau, daga yin waka da wani mawakin Jos, Classiq, shikenan sai aka fara sukar ta da ya kai ga har dakatar da ita akayi sannan akayi ta yi mata raddi akai.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel