Dalilai 5 da suka haddasa wa Obasanjo kiyayya ga Buhari

Dalilai 5 da suka haddasa wa Obasanjo kiyayya ga Buhari

Kamar yadda kuka sani tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na adawa da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan adawa ta sa a watan Janairu ya aikema shugaban kasar da wata wasika inda yake bayyana gazawar gwamnatinsa tukuru.

Harma ta kai ya shawarce shi da kada ma yayi tunani yin tazarce a zaben 2019. Sannan kuma a kwanan nan ya jaddada cewa yana nan akan matsayarsa.

Hakan ya biyo bayan jita-jita da akeyi na cewa ya sauko daga dokin kin goyon bayan shugaban kasar.

Dalilai 5 da suka haddasa wa Obasanjo kiyayya ga Buhari

Dalilai 5 da suka haddasa wa Obasanjo kiyayya ga Buhari

Wannan dalili yasa mutane na ganin bah aka kawai bane yasa Obasanjo kin jinin shugaba Buhari. Domin hart a kai ya kafa sabuwar kungiyar adawa.

Ga wasu daga cikin dalilan da ake ganin sune suka haddasawa Obasanjo kin jinin sake takarar Buhari:

1. Saboda an hana shi ko an ki sabunta masa lasisin mallakar rijiyar mai: Wasu rahotanni sun nuna cewa wannan ya na daya daga cikin haushin da Obasanjo ke ji.

2. Saboda yadda Buhari ke tafiyar da gwamnatin sa: Wasikar da Obasanjo ya rubuta wa Buhari ta na dauke da wasu dalilai na rubuta wasikar. Dalilan sun hada da: rashin karfin tattalin arziki, rashin yin katabus a kan mulki, matsalar kuncin rayuwa kamar talauci da fatara, fifita wani sashe ko jinsi a kan wasu, rashin karbar laifi ko kasawa da sauran wasu dalilai.

3. Obasanjo ya so ya jefa ‘yan-barandar sa a cikin wasu mukamai masu maiko a gwamnatin Buhari, amma aka taka masa burki. Da dama na cewa wannan dalilin ma zai iya sa huldar mutunci tsakanin dattawan guda biyu ta yanke.

4. Wasu rahotanni sun nuna Obasanjo ya rika neman a ba shi wasu kwangilolin da aka rigaya aka bai wa wani, ko aka kebe domin wani ko wani kamfani. An ce idan ba a ba shi ba, ran sa ya rika baci sosai.

5. Kwangilar tashar samar da hasken lantarki ta Mambilla. An ce ita ce abu na karshe da ya tunzura Obasanjo har ya rubuta wannan wasika a ranar 23 Ga Janairu, 2018.

KU KARANTA KUMA: Tsawa ya hallaka mutane biyu a jihar Kaduna

Shugabannin kungiyar matasan Arewa sun bayyana cewa zasu gudanar da zaben ba’a ga dukkanin yan takaran shugaban kasa daga Arewa ciki harda shugaba Muhammadu Buhari.

Sauran yan takaran da kungiyar ta lissafo sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe, Tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaaso, Gwamna Aminu Tambuwal da Sule Lamido.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel