Tsige Shugaba Buhari zai kawo koma baya a Najeriya - Gowon

Tsige Shugaba Buhari zai kawo koma baya a Najeriya - Gowon

A ranar da ta gabata ne tsohon shugaban kasar Najeriya Janar Yakubu Gowon, ya yi gargadi kan batun tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewar ko kusa bai dace a fara tunanin aikata hakan ba cikin kasar nan a halin yanzu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Janar Gowon ya yi gargadin cewa muddin aka fara tsige wani shugaba a kasar nan to kuwa son zuciya na kungiyoyi daban-daban ba zai bari wani shugaba yayi tasiri akan kujerar sa ba.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da majalisar ta fara babatun tsige shugaba Buhari dangane da sayen jiragen sama akan kudi na Dalar Amurka miliyan 496 ba tare da neman izinin ta ba.

Tsige Shugaba Buhari zai kawo koma baya a Najeriya - Gowon

Tsige Shugaba Buhari zai kawo koma baya a Najeriya - Gowon

A yayin da yake jawabai ga shugabannin Arewa da masu ruwa da tsaki na majalisar dattawa a ofishin sa dake garin Abuja, Janar Gowon ya bayyana cewa akwai bukatar hadin kai na musamman a yankin Arewa da kuma kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Matasan Arewa za su tantance Shugaba Buhari da sauran 'Yan Takara na Arewa kafin Zabe

Wadanda suka halarci wannan taro sun hadar da tsohon shugaban majalisar wakilai Ghali Umar Na'Abba; tsohon ministan Abuja, Abba Gana; tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu; Sanata Joseph Waku da Sanata Paul Wampana.

Sauran mahalarta taron sun hadar da tsohon mai bayar da shawara akan harkokin siyasa ga Shehu Shagari, Alhaji Tanko Yakasai, Ministar harkokin mata, Hajiya Maryam Chiroma; Zainab Maina da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel