Hotunan Shugaba Buhari yayin dawowar sa daga Kasar Amurka

Hotunan Shugaba Buhari yayin dawowar sa daga Kasar Amurka

A daren ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka a birnin tarayya bayan ziyarar aiki da ya kai kasar Amurka inda ya gana da shugaban kasa, Donald Trump a fadar sa ta White House.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, jirgin da ya yo jigilar shugaban kasa Buhari tare da 'yan tawagar sa ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake garin Abuja da misalin karfe 10.35 na daren jiya.

Wadanda suka tarbi shugaba Buhari filin jirgin saman sun hadar da ministan Abuja; Mallam Musa Bello, shugaban ma'aikata na shugaban Kasa; Mallam Abba Kyari da wasu shugabanni na hukumomin tsaro.

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin 'yan tawagar da suka yi rakiyar shugaban Buhari zuwa Kasar Amurka sun hadar da gwamnan jihar Ogun; Ibikunli Amosun da na jihar Filato; Simon Bako Lalong.

Cikin Ministoci 'yan tawagar shugaba Buhari sun hadar da na harkokin kasashen ketare; Geoffrey Onyeama, Ministan Shari'a; Abubakar Malami da kuma Ministan Kasuwanci da Masana'antu; Okechukwu Enelamah.

KARANTA KUMA: Mutuwar Wani 'Dalibi 1 ta sanya an rufe wata Jami'a a jihar Kano

Rahotannin sun bayyana cewa, sauran 'yan tawagar shugaba kasa sun hadar da; shugabannin kwamitin majalisar wakilai da na dattawa akan harkokin kasashen ketare, shugaban hukumar NIA, Ahmad Rufa'i Abubakar da kuma shugaban dakarun Soji, Janar Aboyomi Olanisakin.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito dalilin tsaiko da shugaban kasa ya samu yayin dawowar sa, inda babban hadimin sa Mista Femi Adesina ya bayyana cewa ya samu tsaiko ne a birnin Landan sakamakon duban lafiya ta jirgin da ya yi jigilar jiga-jigan kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel