Za mu cigaba da kama wadanda su ka saci kudin kasa - Osinbajo

Za mu cigaba da kama wadanda su ka saci kudin kasa - Osinbajo

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta kara tabbatar da kan ta wajen yaki da sata a Najeriya bayan da Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi wani jawabi kwanan nan.

Farfesa Yemi Osinbajo yace Gwamnatin su za ta cigaba da yin ram da Barayin Najeriya ana binciken su. Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana wannan ne lokacin da aka kaddamar da wani tsari na kananan ‘yan kasuwa a Garin Ondo.

Za mu cigaba da kama wadanda su ka saci kudin kasa - Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo a ofis

Mataimakin Shugaban kasar ya nuna cewa duk da Gwamnatin Buhari ba ta samu kudi kamar lokacin tsohon Shugaba Jonathan ba amma sun yi aikin da PDP ba tayi ba. Daga ciki akwai hanyoyi da dama da kuma titunan dogo na jirgin kasa.

Har wa yau Mataimakin Shugaban na Najeriya Yemi Osinbajo yace za a cigaba da tuhumar barayi ko da Kotu ta ki daure su. Farfesa Osinbajo yace ko da ba a daure kowa ba za su yi ta gurfanar da wadanda ake zargi da laifin sata a gaban shari’a.

KU KARANTA: Sanatoci na zargin gidan Sojan Najeriya da badakala

Yemi Osinbajo yace Ubangiji ba zai bar barayi su yi nasara ba a Najeriya, Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewa wadanda su ka saci kasar ne su ke kokarin dawowa mulki domin su cigaba daga inda su ka tsaya amma za ayi maganin su.

Ba dai yau ne Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya fara bayyana irin satar da Gwamnatocin baya su kayi ba. Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo yace ba za su daina maganar ta'asar da PDP tayi a baya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel