‘Yan Majalisa za su kafar wando daya da Hukumar fansho na Sojin Najeriya

‘Yan Majalisa za su kafar wando daya da Hukumar fansho na Sojin Najeriya

- Sanatoci su na zargin akwai cuwa-cuwa a tsarin fanshon Sojin Najeriya

- ‘Yan Majalisar sun ce an kashe wasu Biliyoyi da ba su cikin kasafin bara

- Shugaban Hukumar ya musanya haka yace Majalisar ba ta saurare su ba

Mun samu labari daga Jaridar Daily Post cewa ‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya su na zargin cewa an tafka wata badakala ta Biliyoyin kudi a Hukumar fanshon gidan Sojan Najeriya a Gwamnatin nan ta Shugaba Muhammadu Buhari.

‘Yan Majalisa za su kafar wando daya da Hukumar fansho na Sojin Najeriya

Ana zargin gidan Sojan Najeriya da badakalar Biliyoyi

Wani Kwamitin Majalisar Dattawa yayi bincike inda ya zargi cewa an karkatar da Naira Biliyan 44 a Hukumar lura da fanshon tsofaffin Sojojin Kasar. Shugaban kwamitin Sanata Mathew Uroghide ya bayyanawa Majalisa wannan.

Majalisar ta gano cewa an biya wasu Sojojin kasar da su kayi ritaya kudin fanshon su ne ta wani tsari na SWV a maimakon yadda doka ta tanada. A ka’ida ya kamata a ware wannan kudin ne cikin kasafin kudin Kasar amma ba ayi ba.

KU KARANTA: Bukola Saraki ya caccaki Shugaba Buhari a fili

Sanata Mathew Uroghide a binciken sa yace Akanta-Janar na kasar ya turawa asusun Hukumar fanshon na Sojoji kudi Nara Biliyan 44 daga asusun Gwamnati. A kasafin kudin kasar dai Miliyoyi ne kurum aka warewa Hukumar a bara.

Mathew Uroghide ya nemi jin ta bakin Hukumar amma abin ya faskara domin kuwa sun kasa bayyana a gaban Majalisar. Shugaban Hukumar Janar Adekunle Adigun ya dai karyata wannan magana inda yace Majalisa ba ta saurare su ba da su ka zo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel