Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya da daren nan daga birnin Ingila. Shugaban kasan ya biya Landan ne bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasan Amurka Donald Trump.

Jirgin shugaba Buhari ya dira babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe ne misalin karfe 10:17 na daren nan.

Ya dawo ne bayan mun tuhumci rashin dawowansa tun bayan kwanaki 2 da ya bar Amurka kuma babu wani rahoto daga fadar shugaban kasa da ya fadawa yan Najeriya inda shugaban kasan su ya biya.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel