Mutune 8 sun mutu yayin da tanka makare da mai ta kama da wuta a Arewa

Mutune 8 sun mutu yayin da tanka makare da mai ta kama da wuta a Arewa

Kawo yanzu dai alkaluman da muka samu sun tabbatar mana da cewa akalla mutane takwas ne su ka riga mu gidan gaskiya sannan kuma wasu da yawa suka jikkata bayan da wasu tankoki biyu makare da man fetur suka yi taho mu-gama a garin Zing, na jihar Taraba dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan.

Mun samu cewa dai direban dayan tankar ya na sharara gudu ne biyo bayan wasu sojoji da ke bin sa kafin daga bisani motar ta kufce masa.

Mutune 8 sun mutu yayin da tanka makare da mai ta kama da wuta a Arewa

Mutune 8 sun mutu yayin da tanka makare da mai ta kama da wuta a Arewa

NAIJ.c ta samu haka zalika cewa a wurin kokarin ya karkato motar ta koma kan titi ne ya bugi wata tankar wacce itama ta na dauke da man fetur din kuma tana ta tafiya ne a kan titi.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Enugu sun bayar da labarin samun nasarar lalata sauran boma-boman da 'yan tawayen yankin Biafra suka yi anfani da su a lokacin yakin basasa har guda 15.

Mai magana da yawun rundunar Sufuritanda Ebere Amaraizu shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar ya kuma raba a garin na Enugu.

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel