Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta yi wa Shugaba Buhari kaca-kaca

Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta yi wa Shugaba Buhari kaca-kaca

Hadakar nan ta wasu zaratan 'yan Najeriya da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya assasa da zummar maido da martabar kasar a bisa turba daidaitacciya watau Coalition for Nigeria Movement (CNM) ta yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo.

Hadakar ta Coalition for Nigeria Movement dai kamar yadda muka samu ta na maida martani ne ga shugaban kasar game da kalaman sa a yayin wata fira da yayi lokacin ziyarar sa kasar Amurka game da yadda tsaffin shugabannin kasar Najeriya suka lalata kasar.

Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta yi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta yi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

Legit.ng ta samu cewa hadakar ta CNM ta bayyana takaicin ta ne a kan yadda shugaban a duk inda ya bode baki baya yabon kowa sai kan sa.

A wani labarin kuma, Kamar yadda muka samu labari da dumin sa daga majiyar mu mai tushe na nuni ne da cewa wasu daga cikin shugabannin al'ummar yankunan kudanci da kuma tsakiyar Najeriya sun yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin majalisar dattijan Najeriya.

Kamar yadda muka samu, cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Ayo Adebanjo, Edwin Clark, Obong Victor Attah, Chukwuemeka Ezeife, John Nwodo, da kuma Mr. Yinka Odumakin.

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel