Zaben 2019: Obasanjo bai isa ya hana ni komai ba - Atiku Abubakar

Zaben 2019: Obasanjo bai isa ya hana ni komai ba - Atiku Abubakar

Fitaccen dan siyasar na kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ba ya taba yaba dukkan wani abu idan dai har ba shi ne yayi shi ba.

Fitaccen dan siyasar dake zaman wazirin Adamawa, Alhaji Atiku yayi wannan ikirarin ne yayin da yake mayar da martani ne kan wata tambaya da wakilin majiyar mu Jimeh Saleh ya yi ma sa lokacin firar su a satin da ya gabata.

Zaben 2019: Obasanjo bai isa ya hana ni komai ba - Atiku Abubakar

Zaben 2019: Obasanjo bai isa ya hana ni komai ba - Atiku Abubakar

Legit.ng ta samu cewa tun farko dai an tambayi Atiku din ne ko meye ra'ayin sa dangane da kalaman Obasanjo, inda ya ce ba zai taba barin shi ya shugabanci Najeriya ba matukar yana raye inda shi kuma ya cewa Obasanjo din bai isa ya hana shi ko ya sa ya zama wani abu ba sai abunda Allah ya nufa.

A wani labarin kuma, Kimanin shekaru 28 da suka shude, Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Mista Boss Mustapha ya yi bayanin yadda yace tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya shirya masa kullalliyar da ta hana shi zama Gwamnan Adamawa.

Kamar dai yadda Boss Mustapha din ya ayyana, biyo bayan sabanin da suka samu da fitaccen dan siyasar Atiku lokacin da ya nemi ya kakaba masa mataimaki, sai kawai ya juya masa baya ya hada kai da jam'iyyar adawa.

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel