Da dumin sa: Dattijan 'yan kudanci da tsakiyar Najeriya sun yi ganawar sirri da Saraki da Ekweremadu

Da dumin sa: Dattijan 'yan kudanci da tsakiyar Najeriya sun yi ganawar sirri da Saraki da Ekweremadu

Kamar yadda muka samu labari da dumin sa daga majiyar mu mai tushe na nuni ne da cewa wasu daga cikin shugabannin al'ummar yankunan kudanci da kuma tsakiyar Najeriya sun yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin majalisar dattijan Najeriya.

Kamar yadda muka samu, cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Ayo Adebanjo, Edwin Clark, Obong Victor Attah, Chukwuemeka Ezeife, John Nwodo, da kuma Mr. Yinka Odumakin.

Da dumin sa: Dattijan 'yan kudanci da tsakiyar Najeriya sun yi ganawar sirri da Saraki da Ekweremadu

Da dumin sa: Dattijan 'yan kudanci da tsakiyar Najeriya sun yi ganawar sirri da Saraki da Ekweremadu

Legit.ng ta samu cewa duk da dai har yanzu ba'a san takamaimai me suka tattauna ba a kai, amma dai ana tunanin tatsuniyar gizo ba zata wuce ta koki ba domin kuwa ba za su rasa nasaba da batun tsaro da siyasar kasa ba.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya kuma na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da yake tunanin shine ya sanya 'yan kabilar yarbawa basu zabe sa ba a zaben 1999.

A cewar Cif Obasanjo, yana tunanin saboda ya ki ya shiga kungiyar nan ta hadaddiyar kabilar yarbawan dake kare muradun su ta Afenifere da Marigayi Sanata Abraham Adesanya yake shugabanta a wancan lokacin ne ya janyo hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel