'Yan sanda sun kama wasu mata masu ciki da laifin satar Plasma TV

'Yan sanda sun kama wasu mata masu ciki da laifin satar Plasma TV

- Hukumar 'yan sanda sun kama wasu mata guda biyu da laifin satar talabijin mai kirar Plasma, 'yan sandan sun kama matan ne a ranar Alhamis dinnan, matan wadanda suke dauke da juna masu suna, Mimi Abbas mai shekaru 21 da kuma Sofia Suleiman, mai shekaru 25. An gurfanar da masu laifin a wata babbar kotu dake Karu a cikin birnin Abuja

'Yan sanda sun kama wasu mata masu ciki da laifin satar Plasma TV

'Yan sanda sun kama wasu mata masu ciki da laifin satar Plasma TV

Hukumar 'yan sanda sun kama wasu mata guda biyu da laifin satar talabijin mai kirar Plasma, 'yan sandan sun kama matan ne a ranar Alhamis dinnan, matan wadanda suke dauke da juna masu suna, Mimi Abbas mai shekaru 21 da kuma Sofia Suleiman, mai shekaru 25. An gurfanar da masu laifin a wata babbar kotu dake Karu a cikin birnin Abuja.

DUBA WANNAN: Kachikwu ya maida wa Falana martani akan makudan kudin tallafin mai

Mimi Abbas da Sofia Suleman suna zaune ne a Masaka dake jihar Nasarawa, kotu tana tuhumar su da laifin sata, inda suka ki amincewa da laifin da ake zargin su dashi din. Mai gabatar da kara, Edwin Ochayi, ya shaidawa kotu cewar wata mata mai suna Mrs Favour Eyo da take zaune Airport Road dake birnin Abuja, ta bada tabbacin faruwar lamarin a ofishin 'yan sanda dake Wuse Abuja a ranar 14 ga watan Afirilu, da misalin karfe 11:30 na safe.

Mai gabatar da karar da cewar a ranar 13 ga watan Afirilu, wadanda ake zargin suka kama daki a wani otal, inda suka saci talabijin masu kirar Plasma guda hudu, wanda kudin su ya kai kimanin naira dubu 260.

"Koda yake an gano daya daga cikin talabijin din a kan titin airport road, amma an kama wadanda ake zargin a ranar 15 ga watan Afrilu a Masaka, kuma sun furta cewa sun aikata laifin da ake tuhumar su dashi din," inji Ochayi.

Ya kara da cewa wannan shine karo na biyar da aka kama Sofia Suleman da aikata laifi irin wannan. A cewar mai gabatar da kara, laifin yana karkashin sashe na 79 da kuma sashe na 287 na dokar shari'a.

ALkalin kotun Hassan Ishaq, yace ya bayar da belin wadanda ake tuhumar akan naira dubu 100, tare da shaidu. Sannan alkalin ya bukaci shaidun da su rubuta takarda dake nuna cewar masu laifin baza su sake aikata laifi irin wannan ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel