Kuri'un 'Yan Najeriya su za su tantance sakamakon Zaben 2019 - INEC

Kuri'un 'Yan Najeriya su za su tantance sakamakon Zaben 2019 - INEC

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC, ya bayar da tabbacin sa ga 'yan Najeriya da cewa ko shakka babu kuri'un su ne za su tantance sakamakon babban zabe na 2019.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, shugaban hukumar ya bayyana hakan a wata lacca ga daliban jam'iar Abuja da hukumar ta gudanar kan shirin fadar ka da daliba muhimmancin kuri'un su a zaben kasa na 2019 mai gabatowa.

Farfesan ya bayyana cewa, ya lashi takobbi n tabbatar da kuri'un dukkanin 'yan Najeriya sun taka rawar gani wanje tantance 'yan takara da za su samu nasara a zaben 2019.

Kuri'un 'Yan Najeriya su za su tantance sakamakon Zaben 2019 - INEC

Kuri'un 'Yan Najeriya su za su tantance sakamakon Zaben 2019 - INEC

A sakamakon haka ne jagoran hukumar ya gargadin daliban a yayin gudanar da shirin na wayar da da kai da su tabbatar sun mallakin katin zabe kafin lokaci ya kurace masu.

KARANTA KUMA: Ajali ya Katse Hanzarin Wani Matashi da ya sha ƙwayar Tramol a jihar Benuwe

Farfesa Yakubu ya kara da cewa, ko shakka ba bu matasa su ne makomar kasar nan ta Najeriya, inda ya nemi su akan su tabbatar sun kada kuri'un su da za su taka rawar gani wajen tantance sakamakon zaben.

A na sa jawabin shugaban jami'ar Farfesa Michael Umale Adikwu wanda mataimakin sa ya wakilta, Farfesa EJV Nwanna ya yabawa hukumar INEC dangane da wannan shiri da ta gudanar a jami'ar domin wayar da kai gami da fadakar da dalibai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel