Lauyar Najeriya ta yanke mazakutar mijin ta, ta buge da hauka

Lauyar Najeriya ta yanke mazakutar mijin ta, ta buge da hauka

Wata lauya ta kashe mijin ta ta hanyar yanke masa al'aura sannan ta saka su cikin hannun sa na dama a rukunin gidajen Diamond dake Sango-Tedo a Legas.

'Yan sanda sun bayyana lamarin da ya faru da misaln karfe 7:30 na safiyar yau, Alhamis, da cewar babu kyan gani.

Marigayin, Otike Odibi, dan asalin jihar Delta, wanda shi ma lauya ne, ya auri matar sa, Udeme Odibi, 'yar asalin jihar Akwa Ibom, shekaru uku da suka wuce.

Lauyar Najeriya ta yanke mazakutar mijin ta, ta buge da hauka

Lauyar da ta yanke mazakutar mijin ta

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar, Legas SP Chike Oti, ya ce DPO din su dake Ogomah a Ajah aka fara kira tare da sanar da shi cewar matar Mista Otike Odibi ta kashe shi a gidan su dake unguwar Sango-Tedo.

DUBA WANNAN: Dangote ya yi sabbin nade-nade a kamfanonin sa, duba sunayen su da mukami

"Bayan samun wannan kira ne sai ya ya jagoranci tawagar jami'an sa inda suka je suka iske Mista Odibi cikin jini male-male, an farke cikin sa har ta kai ga ana ganin hanjin sa. Bayan haka kuma ga shi an cire masa mazakuta an saka a hannun sa na dama," a cewar kakakin 'yan sanda Chike Oti.

Saidai kafin zuwan jami'an tsaro uwargida Udeme tayi kokarin kashe kan ta amma hakan bata yiwu ba. Yanzu haka tana asibiti domin duba lafiyar ta.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas, CP Edgal Imohimi, ya bukaci sashen kwararru a bangaren binciken kisa na hukumar 'yan sanda da gudanar da binciken kwakwaf a kan batun kisan.

Lauyar Najeriya ta yanke mazakutar mijin ta, ta buge da hauka

Gawar mijin

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel