Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari na kan hanyar dawowa Najeriya bayan nusanin kwanaki biyu

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari na kan hanyar dawowa Najeriya bayan nusanin kwanaki biyu

A yayin da ake cigaba da cece-kuce a kan batun dawowar shugaba Buhari Najeriya bayan ya baro kasar Amurka da kwanaki biyu, sai ga shi sanarwa ta fito cewar yana kan hanyar sa ta dawowa.

Mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya sanar da hakan da yammacin yau, Alhamis.

Tun da farko, mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana cewar shugaba Buhari ya tsaya a birnin Landan ne domin a duba lafiyar jirgin sa sannan a kara masa mai.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari na kan hanyar dawowa Najeriya bayan nusanin kwanaki biyu

Shugaba Buhari na kan hanyar dawowa Najeriya bayan nusanin kwanaki biyu

A yau ne kafafen yada labarai suka fara wallafa rahotannin neman inda shugaba Buhari ya ke bayan ya bar kasar Amurka, inda ya amsa gayyatar shugab Trump.

DUBA WANNAN: An samu canje-canje a shugabancin kamfanin Dangote, duba sabbin nade-naden da aka yi

Bada dadewa ba shugaba Buhari ya ziyarci kasar Ingila inda ya halarci taron kasashen Common Wealth.

Shugaba Buhari ya shafe watanni a shekarar 2017 da ta wuce a kasar Ingila inda ya yi zaman jinya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel