Dino Melaye: Ba za mu cigaba da kallo ana yi mana wulakanci ba – Dogara

Dino Melaye: Ba za mu cigaba da kallo ana yi mana wulakanci ba – Dogara

- Yakubu Dogara yayi tir da abin da ke faruwa da Dino Melaye

- Majalisa tace babu gaira babu dalili aka taso Sanatan a gaba

- Dogara ya nemi Shugaban ‘Yan Sanda ya sa baki a maganar

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara yayi magana game da batun Sanatan Najeriya Dino Melaye inda ya nemi ‘Yan Sandan kasar su tabbatar da koshin lafiyar sa ya kuma nemi IG ya duba lamarin.

Dino Melaye: Ba za mu cigaba da kallo ana yi mana wulakanci ba – Dogara

Shugaban Majalisa Dogara yayi Allah-wadai da abin da ya faru da Melaye

Majalisar Wakilan Tarayya ta sa baki a maganar Sanata Dino Melaye wanda tace an taso gaba ne saboda matsayar sa a Kasar. Yakubu Dogara yace ba za su yi tsit ba su na gani, kuma ya nemi ‘Yan Sanda su kula da Sanatan.

Shugaban Majalisar Wakilan kasar Rt. Hon. Yakubu Dogara ya nemi Sufeta Janar na ‘Yan Sandan kasar ya shigo cikin maganar. Dogara yace ba za su tattauna batun ba saboda maganar tana gaban Sanatocin kasar a yanzu haka.

KU KARANTA: Sanatan Bayelsa ya bayyana abin da ya faru da Dino Melaye

Rt. Hon. Yakubu Dogara yayi kira ga Jami’an tsaro da su fara duba lafiyar Sanata Dino Melaye kafin a fara maganar maka shi a Kotu domin lafiyar sa ce a gaba. Wani ‘Dan Majalisa daga Kogi Sunday Karimi ya tado maganar dazu.

Kun ji labari cewa dai yau aka gurfanar da Sanatan a gaban Kotu inda ake ki bada belin sa. Yakubu Dogara yace bai ga dalilin kinkimar mutumin da ke kwance zuwa Kotu ba don kuwa ko magana ba zai iya ba a gaban shari’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel