Matasan Arewa za su tantance Shugaba Buhari da sauran 'Yan Takara na Arewa kafin Zabe

Matasan Arewa za su tantance Shugaba Buhari da sauran 'Yan Takara na Arewa kafin Zabe

Wata Kungiyar matasan Arewa ta Arewa Consultative Youths Movement (ACYM), ta bayyana cewa za ta gudanar da wani nau'in zaben tantance 'yan takara na Arewa masu neman kujerar shugaban kasa domin tabbatar da mashahuri kafin zaben 2019.

Jagoran Kungiyar, Alhaji Kabiru Yusuf, shine ya bayyana haka yayin ganawar ranar Alhamis ta yau tare da manema labarai a birnin tarayya na Abuja.

Alhaji Kabiru wanda a kwana-kwanan aka sake zabar sa a matsayin jagoran kungiyar ta ACYM ya bayyana cewa, 'yan takarar da kungiyar za ta tantance sun hadar da shugaban kasa Muhammadu Buhari, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato

Sauran mafi shahara cikin 'yan takarar da kungiyar za ta tantance sun hadar da; gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo, tsohon shugaban jam'iyyar PDP Alhaji Ahmed Makarfi da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Ambasada Sule Lamido.

Matasan Arewa za su tantance Shugaba Buhari da sauran 'Yan Takara na Arewa kafin Zabe

Matasan Arewa za su tantance Shugaba Buhari da sauran 'Yan Takara na Arewa kafin Zabe

Shugaban ya bayyana cewa, kungiyar za ta aiwatar da wannan zabe ne kan 'yan takarar domin tantance mashahuri cikin su mai manufa ta cikar burikan matasa da za ta samu madogara ta mara masa baya a babban zabe na 2019.

KARANTA KUMA: Guguwar Iska ta kashe Mutane 76 a Kasar Indiya

Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar za ta gudanar da wannan tantancewa ne a shafin ta na yanar gizo da zai dauki tsawon kwanaki 60 ta na aiwatar wa kafin ta sanar da mashahurin gwarzon matasan kasar nan.

A yayin haka kuma shugaban ya kirayi daukacin matasan kasar nan akan su tabbatar da mallakar katin zabe da zai ba su damar kada kuri'u a babban zabe na 2019.

Shugaban ya kara da cewa, lokaci ya karato da ya kamara matasa su tabbatar da sun zabi jagora managarci domin dukkannin wadanda suka shude a baya sun gaza.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel