NDPHC: Majalisar Dattawa ta nemi a maida wanda aka kora daga aiki a ofis

NDPHC: Majalisar Dattawa ta nemi a maida wanda aka kora daga aiki a ofis

- Sanatoci sun nemi a maida wata da aka kora daga ofis aikin ta

- Kamfanin wuta ta sallami wata bayan tayi shekaru 24 tana aiki

- Bincike ya nuna cewa sallamar da aka yi mata ya sabawa ka’ida

Mun samu labari cewa Majalisar Dattawan Najeriya sun nemawa wata da aka sallama daga aiki hakkin ta bayan wani dogon bincike da ake yi tun bara da wani kwamiti na Sanatocin ya gudanar kwanaki.

NDPHC: Majalisar Dattawa ta nemi a maida wanda aka kora daga aiki a ofis

Sanatan APC ya nemi NDPHC ta dawo da wata Ma'aikaciya aiki

Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto cewa Majalisar Tarayyar tayi kira da a maida daya daga cikin tsofaffin Shugabannin Kamfanin wuta na NDPHC watau Misis Maryam Danna Mohammed ofishin ta cikin gaggawa.

Majalisar ta cin ma wannan matsaya ne bayan wani bincike da kwamitin jin korafin jama’a ya gudanar kwanaki. Sanata Baba Kaka Garbai na Jam’iyyar APC mai wakiltar Yankin Jihar Borno ne ya jagoranci wannan bincike.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya tsaya a Landan domin yayi wa jirgin sa fashi

Sanatan na Borno ta tsakiya ya bayyanawa Majalisa cewa Maryam Danna Mohammed tana cikin wadanda aka kora daga aiki a Kamfanin wutan a 2016. Sai dai koran ya sabawa ka’ida Inji Sanatan na Jihar Borno ta tsakiya.

Wannan Baiwar Allah tayi aiki tun kamfanin yana NEPA har ya dawo PHCN wanda daga baya ya koma hannun NDPHC sai dai kwatsam aka kore ta bayan shekaru 24 tana aiki don haka Majalisa ta nemi a dawo da ita bakin aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel