Dangote ya yi sabbin nade-nade a kamfanonin sa, duba sunayen su da mukami

Dangote ya yi sabbin nade-nade a kamfanonin sa, duba sunayen su da mukami

Kamfanin Dangote ya sanar da sabbin nade-naden wasu mutane a wasu mukamai domin kara inganta aiyukan rukunin masana'antun sa.

Mista Olakunle Alake, shugaban sashen aiyuka na rukunin kamfanonin Dangote, ya zama sabon shugaba na kamfanonin Dangote.

Dangote ya yi sabbin nade-nade a kamfanonin sa, duba sunayen su da mukami

Dangote ya yi sabbin nade-nade a kamfanonin sa, duba sunayen su da mukami

An karawa Dakta Adenike Fajemirokun girma daga matsayin babbar darakta a sashen kididdigar asara ya zuwa ofishin shugaban inda zata cigaba da wasu aiyuka na musamman bayan aiyukan ofishin ta.

KU KARANTA: Majalisa na goyon bayan karin albashi mafi karanci ga ma'aikatan Najeriya - Dogara

Ita ce mace ta farko da ta taba taka mukamin babbar darekta a rukunin kamfanonin Dangote.

An nada Mista Austine Ometoruwa a matsayin babban darektan kudi da ajiya.

Da yake magana a kan sabbin nade-naden, Aliko Dangote, ya bayyana cewar ya yi matukar farinciki da samun mace a babban matsayi tare da bayyana cewar kamfanin Dangote na kula da hakkin kowa da kowa.

Dakta Fajemirokun tayi aiyuka a wurare da dama da suka hada da Goldman Sachs a London da Amurka, Deutsch Bank a nahiyar Turai, First Bank da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel